Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta soki ƙudurin da majalisa ta gabatar kan lasisin su.

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta soki ƙudurin da Majalisar wakilan ƙasar ta gabatar da ke neman tilasta wa likitoci aikin shekara biyar kafin samun lasisi.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taron gaggawa na shugabanninta, ta bayyana adawarta ga ƙudurin.

Sanarwar ta ce ƙungiyar ta yi mamaki game da wanda ya gabatar da ƙudurin Honourable Ganiyu Johnson.

Haka kuma kungiyar ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashi da ta ce gwamnatin tarraya ba ta yi wa wasu daga cikin mambobinta ba, a yayin da wa’adin gwamnatin ke zuwa ƙarshe.

Ƙungiyar ta ce ta damu kan yunƙurin majalisar wakilan na tilasta wa likitoci abin da ta kira da ”karin zangon shekara biyar bayan karatun digiri” kafin a ba su lasisi, ko a bar su su fita zuwa ƙasashen waje idan suna da sha’awar yin hakan.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan sake duba albashin mambobinta da tacegwamnatin tarayya ta gaza yi, duk kuwa da irin tarin alƙawuran da kungiyar ta ce gwamnatin ta sha yi musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *