‘Yan bindiga sun sace mutane 80 a Zamfara

Akalla mutane 80 ne ‘yan bindiga suka sace a kauyen Wanzamai da ke jihar Zamfara a shiyar arewa maso
yammacin Najeriya.

Mutanen da suka hada da kananan yara masu shekaru daga 12-17 da mata an sace su ne a jiya Juma’a a lokacin da suke aikin gyaran gona a cewar wani magidanci mai suna Musa Usman da shi ma aka sace yaronsa dan shekaru 14 da haihuwa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da sace mutanen, inda ya kara da cewa a halin yanzu suna aiki tare da sojoji domin ganin an kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.

Jihar Zamfara dai ta jima tana fama da hare-haren wadannan ‘yan bindiga da ke sace mutane su yi garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *