“Wasu ƴan barandan siyasa na barazana ga tarihin Najeriyada na al’ummarta” – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce wasu ƴan barandan siyasa na barazana ga tarihin Najeriya da na al’ummarta.

A cikin wani saƙon taya murna na bukin Easter da Sarkin Musulmin ya aika wa shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, ya ce lamarin ‘aiki ne na Shaiɗan, wanda makircinsa mai rauni ne.’ Kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana.

A cikin jawabin nasa, wanda ya samu sa hannun Mataimakin shugaban Majalisar Ƙoli ta Lura da Harkokin
Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu, Sarkin ya buƙaci shugaban na CAN ya haɗa hannu da
Ƙungiyar ta Musulunci wajen ganin an rage yadda limamai da fastoci ke cusa wa mabiyansu ƙiyayya ta siyasa da kuma munanan kalamai.

Daga ƙarshe mai alfarma Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar Easter tare da
addu’ar ci gaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *