Marayu 290 sun anfana ta tallafin kayan sallah da kungiyar tallafawa marayu ta saba rabawa

Kimanin marayu 290 ne suka anfana ta tallafin kayan sallah da kungiyar tallafawa marayu da marasa hali ta unguwar Ja’oji ta saba rabawa ga marayun da ke yankin Ja’oji da kewaye.

Uban Kungiyar Umar Usain ya bayyana hakan bayan rabon kayan inda yace duk da halin rashi da ake ciki sun yi bakin kokarinsu wajen rabon kayan kamar yadda suka saba a duk shekara.

Usaini ya ce suna samun kudin shiga ne ta hanyar ware wani adadin kudi da kowanne mamba na Kungiyar ke bayar sannan wasu cikin mazauna unguwar suma suna bada tasu gudunwar a duk shekara domin tallafawa marayun.

Da yake nasiha akan muhimmancin tallafawa marayu limamin masallacin Ja’oji Malam Maje Safiyan ya jaddada kira akan muhimmancin tallafawa marayu da kuma alfanun da hakan ke dashi cikin alumma.

Malam Maje ya kuma bukaci mazauna unguwar Ja’oji da su dinga taimakawa marayun dake unguwar da abin da Allah ya hore Mudu.

Akarshe marayun da suka amfana da tallafin sun bayyana farincinsu bisa yadda Kungiyar ta tallafa musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *