Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata, matar hamshamin dan kasuwar nan mai taimakon jama’a a Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata.

Shugaban, a cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce za a tuna da marigayiyar bisa tausayawa da taimakon da take yiwa marasa galihu.

Inda yace Hajiya Rabi tana da sha’awar hidimtawa mutane, tare da son raba duk Wani abin da take da shi.

Shugaban ya bayyana rayuwarta a matsayin mai sauki da tausayi tare da kasance abin koyi ga duk wadanda ke kewaye da ita.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi ayyukanta na alheri, ya kuma bai wa iyalan Dantata ikon jure wannan rashi da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *