Rundunar ‘Ƴan Sanda ta hana yin tashe a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da gudanar da al’adar gargajiya na watan Ramadan da aka fi sani da Tashe a cikin babban birnin jihar. Tashe wasan al’ada ne mai ban dariya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da gudanar da bukukuwan gargajiya na watan Ramadan da aka fi sani da Tashe a cikin babban birnin jihar.

Rahma ta tattaro cewa Tashe wani wasan nishadi ne na gargajiya na ban dariya da ake gudanarwa tun daga ranar 10 ga watan Ramadan har zuwa karshensa.

A lokacin, Musulmai, yawanci yara da matasa, suna sanya tufafin ban dariya da kuma yin wasan kwaikwayo daban-daban a cikin gidaje da wuraren taruwar jama’a a cikin birni kuma suna samun sadaka daga jama’ar.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta bakin kakakinta, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanar da cewa an dakatar da wasan a fadin jihar.

A cewarsa, dalilin da ya sa aka dakatar da aikin shi ne saboda “masu aikata laifuka suna fakewa da sunan tashe wajen tada hankula/bikin Tashe don aiwatar da muggan laifuka, kamar su ‘yan daba, fashin wayar hannu, barna da shaye-shayen miyagun kwayoyi.”

Ya ce duk wanda aka kama yana karya hakan za a kama shi kuma a hukunta shi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Hakazalika, rundunar ta sake nanata dokar hana hawan doki (Kilisa) ba bisa ka’ida ba da kuma amfani da wasan wuta (Knock-out ko Bangers), tana mai cewa za a kama wadanda suka karya dokar kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.

An yi kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa jiha da kasa addu’a, kuma su ci gaba da taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani mutum ko wani abu ko motsi da ba’a amince da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *