Sarkin Kano ya nada sabbin hakimai

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sake nada wasu sababbin Hakimai guda hudu tare da daga Darajar wasu Hakimansa guda shida.

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancanta da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Wadanda aka nada din sun hadar da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.

Sai kuma Hakiman da aka ciyar dasu gaba sun hada da Malam Umar Sunusi Bunun Kano ya koma Dan Makwayon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.

Saura Hakiman da aka ciyar dasu gaba sune Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zannan Kano zuwa Dan Madamin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikinsu da gaskiya da rikon amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *