Bankin Duniya: Darajar naira ta faɗi da kaso 10%

Bankin Duniya ya bayyana cewa darajar Naira ta samu raguwar da kashi 10.2 cikin 100 a shekarar 2022.

Bankin na Duniya ya danganta tashin farashin kayan abinci da man fetur a duniya da kuma faduwar darajar canjin a matsayin babban abin da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki a yankin kudu da hamadar Sahara. 

Hakazalika, cibiyar bayar da rancen kudi ta lura cewa kudin Cedi na Ghana shi ma ya fuskanci faduwar darajar kusan kashi 40 cikin 100 kuma ya raunana karin kashi 20 cikin 100 ya zuwa wannan shekarar 2023.

Sauran kudaden da suka yi asara mai yawa a bara sun hada da na Sudan (kashi 23.6), Malawi (kashi 20.7), Gambia (kashi 14.6), da Najeriya.

Sai dai kuma ga Najeriya, Bankin Duniya ya bayyana cewa an samu hako mai a karshen shekarar 2022 inda ya ce inganta tsaro ya taimaka wajen hana ci gaba da satar mai amma har yanzu yawan man da ake hakowa yana kasa da kason kungiyar OPEC+.

An kuma lura cewa a cikin watan Janairun 2023, yawan man da ake hakowa ya karu zuwa ganga miliyan 1.34 a kowace rana, amma har yanzu wannan abin da ake fitarwa bai kai kasa da adadin OPEC+ na kasar ba.

A cewar Bankin na Duniya, a yankin yammacin Afirka da tsakiyar Afirka, bayanai sun nuna matsakaicin ci gaban da aka samu a farkon wannan shekara, sakamakon kalubalen da ake fuskanta daga matsi na kasafin kudi, a cikin rashin isassun kudade da kuma matsayin basussuka, da kuma hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya shafi manyan kasashe a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *