Hukumar sadawar ta kasa NCC a, ta nesanta kanta daga zargin da wasu keyi na cewa tana da hannu wajen kwarmata sautin muryar da aka ji ta dan takarara shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi da Bishop David Oyedepo suna tattaunawa.
Cikin tattaunawar ta wayar tarho, an ji Obi yana neman Bishop Oyedepo da ya taimaka masa wajen samun kuri’un Kiristocin yankin tsakiyar arewacin Najeriya, inda ya kwatanata lamarin da “yaki na addini.”
Tun a karshen mako da sautin muryar ya fita ake ta ce-ce-ku-ce akai a Najeriyar.
Yayin da magoya bayan Obi suke ikirarin hada sautin akayi don a bata masa suna, wasu na cewa da ma Obi mutum ne mai nuna banbancin addini.
Sai dai yayinda wasu ke zarginta da kwarmata sautin, hukumar ta NCC ta nesanta kanta da lamarin tana mai cewa, hakan ya saba dokar aiki.
Cikin wata sanarwa da NCC ta fitar dauke dasa hannun Darektan yada labarainta Reuben Muoka, hukumar ta musanta taka wata rawa a fitar da sautin.
Kakakin NCC ya kara da cewa, hukumar ta kai rahoton wannan zargi da ake mata ga jami’an tsaro domin su gudanar da bincike su kuma dauki mataki idan ya zama dole.