Hajiya Ladi ta rasu

Hajiya Ladi Audu Bako, matar tsohon Kwamishinan ‘yan sanda kuma Gwamnan Kano a mulkin soja daga 1967 zuwa 1975 ,Marigayi Alhaji Audu Bako ta rasu.

Hajiya Ladi Audu Bako ta rasu ne a safiyar ranar Laraba 5 ga watan maris 2023, tana da shekaru 93.

Rasuwar Tata ta biyo bayan gajeriyar rashin lafiya da ta yi, wadda har ta kai ta ga kwanciya a Asibiti.

Za a yi jana’izarta da misalin karfe 2:00 na rana a yau laraba a fadar Sarkin Kano kamar yadda diyarta Zainab Audu Bako ta bayyana.

Tuni aka yi mata jana’iza a fadar Sarkin Kano dake Kofar Kudu.

Hajiya Ladi mahaifiya ce ga shugabar matan jamiyyar PDP ta shiyyar Arewa maso yamma cin kasar nan, Hajiya Zainab Audu Bako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *