A karon farko tun bayan mamayar Rasha, Zelensky ya kai ziyara Poland.

A karon farko tun bayan mamayar Rasha, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya kai ziyara Poland.

Poland na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi magana da kuma bayar da cikakken goyon baya ga Ukraine tun da aka fara yaki.

Ta karɓi bakuncin miliyoyin ‘yan gudun hijira daga Ukraine, sannan ta aike mata da tankunan yaki fiye da 300.

Kazalika ita ce ƙasar farko davta aike wa Ukraine jiragen yaki. Mr Zelensky ya gode wa al’ummar ƙasar a fadar ƙasar da ke Warsaw. Ya yi bayani a kan yankunan da har yanzu ake zaman ɗar-ɗar a ƙasarsa.

Manoman Poland sun nuna fushinsu a kan yadda ake shigar da hatsin Ukraine cikin kasarsu inda suka ce yana karya farashin nasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *