Majalisa ta Umarci DSS su kama masu shirin kafa gwamnatin rikon kwarya

Majalisar wakilai ta yi Allah wadai da shirin wasu yan siyasa na kafa gwamnatin rikon kwarya tare da bada izini ga DSS su kama..

Majalisar wakilai ta yi Allah wadai da tattaunawa batun samar da gwamnatin rikon kwarya da wasu ‘yan siyasa suka yi.

Rahma ta tattaro cewa An yi Allah wadai da hakan ne a ranar Talatar ban bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP mai wakiltar Akwa-Ibom Unyime Idem ya gabatar.

Idan dai ba a manta ba a wata sanarwa da hukumar ta DSS ta fitar ta ce ‘yan Najeriya su dauki barazanar gwamnatin wucin gadi da muhimmanci.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, sai dai wadanda suka koka da sakamakon zaben sun nuna damuwa.

Mista Unyime yayin da yake gabatar da kudirin, ya ce ‘yan siyasa suna karfafa wadanda suka ji ba dadi da su yi kira da a yi “wanda ba bisa ka’ida ba“.

Ya bayyana gwamnatin rikon a matsayin mara bin tsarin dimokuradiyya, ba bisa ka’ida ba kuma ba a doran dokokin Najeriya ba.

A nasa gudunmuwar, Sergius Ogun ya roki hukumar DSS da ta kama wasu masu hada baki da suka kulla makarkashiyar kafa gwamnatin rikon kwarya a Najeriya.

Kuna ɓata lokacinmu mai daraja kuna gaya mana mu la’ance shi. Idan har wannan gwamnati tana raye ta sauke nauyin da ke kanta wannan bai kamata ma ya zama batun da za mu bari a cikin wannan majalisa ba,” inji shi.

Mataimakin shugaban majalisar, Idris Wase ya shiga tsakani, yana mai cewa “kame wadanda ake zargi da kulla makircin zai haifar da rikicin siyasa“.

Ya bayyana cewa dole ne ‘yan siyasa su shiga cikin jami’an tsaro domin dakile shirin da ka iya kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya.

Saboda kyawawan dalilai, ku fahimci cewa muna karkashin tsarin dimokuradiyya lokacin da suke ambaton hakan – halin da muka samu kanmu, dole ne mu yi magana da kanmu don tabbatar da cewa an yi abin da ya dace,” in ji shi.

 Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Don haka majalisar ta umarci jami’an tsaro da su kasance cikin shiri domin dakile yiwuwar tabarbarewar doka da oda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *