Kotu ta tasa keyar wani matashi a Kano zuwa gidan yari bisa laifin zamba

An gurfanar da wani matashi agaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta a unguwar Kwana huɗu a jihar Kano , bisa jagorancin mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad.

Ana tuhumar matashin da laifin zamba cikin aminci, salwantar da dukiya da kuma salwantar da muhimman takaddu na kuɗi, wanda hakan ya saɓawa sashi na 203,195 da 324 na kundin SPCL.

Tunda fari wani mai suna Idris Musa Yusif ne ya buɗe wa , wanda ake zargin shago a kasuwar Kantin Kwari , bisa yarjejeniya amma sai aka nemi takaddun shagon aka rasa da wasu muhimman kayayyaki.

Wanda ake zargin mai suna Mohd Sani Nasidi mazaunin unguwar Kabuga, ana kuma zargin sa da salwantar da kuɗi sama da naira miliyan goma sha tara.

Mai gabatar da ƙara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa ƙunshin tuhumar da ake yi masa wanda nan ta ke ya musanta zargin.

Lauyan wanda ake tuhuma ya yi roƙi kotun da ta sanya wanda yake kare wa a hannun beli , sai dai masu gabatar da ƙara sun yi suka kan roƙonsu , wanɗan suka roƙi kotin ta basu wata rana dan su gabatar da hujjojinsu kan roƙon belin da suka yi.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya ɗage ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu 2023 dan ci gaba da sauraran shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *