Hadarin mota ya kashe mutum 3 a hanyar gidan gwamnatin Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar da rasuwar mutum uku sakamakon wani hatsarin mota da ya auku da safiyar Talata a birnin Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa hatsarin ya auku ne a kan gadar sama da ke kan hanyar zuwa gidan Gwamnatin jihar.

Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar leta-hayis wacce ta taso daga garin Ajingi ta shiga cikin garin Kano, inda a nan ne murfinta ya daki wani bangaren gadar saman.

Hakan a cewar Kakakin hukumar, ya sa motar ta kama da wuta bayan murfin ya fice daga jikinta..

A cewar Saminu, bayan aukuwar hatsarin, jami’ansu sun je wurin inda suka kwashe gawarwaki tare mutanen da suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka tabbatar da rasuwar mutum uku.

Ya ce yanzu haka ragowar wadanda suka jikkata suna can a asibitin suna samun kulawar gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *