Ganduje Ya Nada Farfesa Jega Shugaban Jami’ar Sa’adatu Rimi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya nada tsohon shugaban Hukumar Zabe ta kasa INEC, Farfesa Muhammad Attahiru Jega a matsayin uba ga sabuwar Jami’ar Nazarin Koyar da Aikin Malinta ta Kano, wato Sa’adatu Rimi University of Education, Kumbotso.

Kazalika Gwamnatin ta Kano, ta amince da nada Oba Dr. Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo a matsayin Shugaban Majalisar Kula da Ayyukan Jami’ar.

Gabanin zama shugaban hukumar zabe, Farfesa Jega ya shugabanci Jami’ar Bayero Kano tsawon shekaru biyar, haka kuma kafin haka, ya kwashe shekaru da dama yana koyar da ilimin kimiyyar siyasa a Jami’ar ta Bayero.

Kwamishinan Labaru na Gwamnatin Kano, Malam Mohammed Garba wanda ya sanar da haka bayan zaman mtajalisar Zartarwa ta jihar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a ranar lahadi, ya ce a kwanan nan ne hukumar kula da Jami’o’I ta Najeriya wato NUC ta amince da daga likafar Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, wato Sa’adatu Rimi College of Education zuwa matsayin Jami’ar nazarin Koyon Aikin Malinta wato University Of Education.

Kwamishinan ya ce sauran mambobin majalisar kula da ayyukan sabuwar Jami’ar sun hada da Dr. Muhammad Adamu Kwankwaso da Hajiya Zulaiha U.M Ahmed da Dr. Ibrahim Yakubu Wunti Dr. Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabiu Bako.

A cewar Kwamishinan, Majalisar zartarwar ta Kano ta amince da nada shugabannin da zasu tafiyar da ayyukan Jami’ar na yau da kullum, wadanda suka hada da Farfesa Isa Yahaya Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar da Kabiru Ahmed Gwarzo mataimakin shugaba mai kula da al’amuran karatu da Dr. Miswaru Bello mataimakin shugaba mai kula da harkokin mulki sai kuma Saminu Bello babban magatakarda na Jami’ar.

Sauran sune Hajiya Mabruka Abubakar Abba shugabar sashin kula da dakunan karatu na Jami’ar yayin da aka nada Ibrahim Muhammad Yahaya babban Jami’in kula da al’amuran kudade.

Ita dai sabuwar Jami’ar nazari da koyon aikin Malinta ta Sa’adatu Rimi dake Kano, ita ce ta 61 a jerin Jami’o’I Mallakar Jihohi yayin da ta kasance ta 222 a jerin Jami’o’in Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *