Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Abdullahi Ibrahim Rogo a matsayin shugaban tsare tsare na lokacin mika mulki.

Mun tattaro cewa Wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin mika mulki na gwamnan jihar Kano 2023 na jam’iyyar NNPP Dr. Abdullahi Baffa Bichi ta nuna cewa nadin zai fara aiki nan take har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce nadin nasa ya samo asali ne a bisa tarihi da jajircewarsa da kuma biyayyarsa daga 2019 zuwa 2023.

‘’Rogo ya kammala karatun kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja. Ya yi wasu karatuttukan da suka hada da Advance Diploma, Professional Diploma da Diploma in Public Administration daga Jami’ar Bayero ta Kano,” inji sanarwar.

Sabon Shugaban tsare-tsaren da aka nada ya rike mukaman siyasa da dama kamar Sakataren Kwamitin riko na rusasshiyar jam’iyyar ANPP na karamar hukumar Dawakin Kudu, mai ba shugaban karamar hukumar shawara na musamman kan harkokin filaye, Sakataren karamar hukumar Rogo, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Rogo mamba a Majalisar Dokokin Jihar Kano.”

 Jaridar Solacebace ta ruwaito cewa Kafin nadin nasa Abdullahi Ibrahim Rogo shi ne sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *