Shugaban NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ya mika takardar murabus din sa daga shugabancin jam’iyyar.

Alkali, wanda ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa sakataren jam’iyyar na kasa, ya yanke shawarar barinsa ne a kan bukatar samar da sabbin hannaye da za su shigo domin gina nasarorin da aka samu a cikin dan kankanen lokaci da ya rike. 

Shugaban jam’iyyar na kasa, ya ce “Bayan abubuwan da suka faru a baya, lokacin da kuma bayan babban zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, 2023, ra’ayi ne na tawali’u cewa jam’iyyarmu ta NNPP tana da kyakkyawar makoma da kuma damar da za ta iya fitowa a matsayin babbar jam’iyyar siyasa da za ta iya zama babbar jam’iyyar siyasa. Kuma dan takarar mu zai iya lashe zaben shugaban kasa da dukkan sauran zabuka a 2027.”

“Tunda a matsayinmu na jam’iyya dukkanmu mun yi imani kuma muna da burin ganin mun samar da ingantacciyar Najeriya ta hanyar hazikin jagorancin jagoranmu, mai girma Sanata Rabi’u Kwankwaso, na yi imanin babu wata sadaukarwa da ta fi karfin kowannenmu.”

“Na tabbata dole ne wannan canjin ya faro daga gare ni.”

“Wannan shi ne dalilin da ya sa na yanke shawarar, tare da duk wani nauyin da ya rataya a wuyan, na fice daga ofishin shugaban jam’iyyarmu ta kasa, don ba da dama ga sabbin hannaye da za mu karbe don ginawa tare da inganta ingantaccen gudunmawar da muka bayar.”

Gwamnatin jihar Kano ta shirya taron addu’oi ga gwamnonin da aka zaba a kasar nan dama sauran shugabanni da kasa baki daya.

Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci taron addu’ar na makaranta al’qur’ani wanda ya gudana a dakin taro na Afirka House dake gidan gwamnatin Kano a yammacin asabar dinnan, inda yace bisa al’ada sun saba shirya taron yin addu’a a jihar nan don neman dorewar zaman lafiya da karuwarb arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *