Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Watanni 8 bayan kai hari ga gidan yarin kuje dake Abuja, rahotanni na cewa har kawo yanzu akwai fursunoni 460 da suka tsere ba tare da an kamasu ba.

Jaridar the punch ta gano bayanan fursunonin a ranar juma’a ta hannun hukumar kula da gidajen yari ta kasa.

Idan za’a Iya tunawa dai an kai harin gidan yarin na Kuje a ranar 5 ga watan Ulin a shekarar 2022, abinda yayi sanadiyyar tserewar fursunoni da dama cikinsu har da yan ta’addar boko haram 64.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewar an samu damar sake kama mutane 421 da suka tsere, Inda aka watsa bayanan sauran fursunonin da ba’a samu nasarar kamawa ba ga yan sandan dake kula da yan ta’adda na duniya.

Idan za a iya tunawa, sama da fursunoni 900, ciki har da manyan ‘yan ta’addan Boko Haram 64, sun tsere daga gidan yari a ranar 5 ga Yuli, 2022.

Sa’o’i kadan bayan haka, kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’esh a yammacin Afirka ta dauki alhakin kai harin tare da fitar da wani faifan bidiyo domin dakile ikirarinta.

Daga bisani jami’an tsaro sun fara farautar wadanda suka tsere, inda aka sake kama wasu kimanin 421

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *