Ganduje ya kafa kwamitin mika wa magajinsa mulki

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da kafa kwamitin mambobi 17 domin mika wa magajinsa mulki.

Haka kuma, Gandujen ya amince da kafa wani karamin kwamiti mai mutm 100 wanda za a fitar da bayanai daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin Jihar Kano.

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Dabo.

Malam Garba ya ce nadin kwamitin ya biyo amincewar Majalisar Zartarwa ta Jihar yayin taronta na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke Fadar Gwamnatin Kano.

Sanarwar ta ce ana sa ran zababben gwamnan jihar zai ba da wakilai uku a babban kwamitin mai mambobi 17.

Ya ce kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji yana da mambobi da suka hada da Shugaban Ma’aikatan Gwamnati da Lauyan Koli kuma Kwamishanan Shari’a da Kwamishinan Yada Labarai da Kwamishinan Muhalli da Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu.

Sauran sun hada da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi da kwamishinan kananan hukumomi da kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa da kwamishinan kudi da kwamishinan ilimi da Darakta-Janar, ofishin kula da filaye da Darakta-Janar na bincike da Manajan Darakta, Tsare-tsare na Birane da sauransu da Hukumar Raya Kasa.

Yayin da Babban Sakatare da Binciken da Harkokin Siyasa, REPA zai zama sakataren kwamitin.

Malam Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin hadin kai da nufin rubutawa tare da mika rahoton mika mulki na karshe cikin makonni uku.

Kwamishinan ya bayyana cewa an bai wa babban kwamitin rikon kwarya umarnin fara shirin mika mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki karo biyu na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce kwamitin zai kuma samu tare da tantance rahotanni daga ma’aikatun gwamnati dangane da manyan nasarorin da aka samu, gami da ayyuka da tsare-tsare da ke gudana dangane da matakin aiwatar da Kasafin Kudi da sauransu daga ranar 25 ga Mayu zuwa yanzu.

Malam Garba ya yi nuni da cewa, an dora wa kwamitin alhakin daidaitawa da gudanar da ayyukan karamin kwamitin kan mika mulki, tattarawa da hada rahotonsu tare da rubutawa da mika rahoton mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin makonni hudu bayan kaddamar da shi.

Ya ce Gwamna Ganduje zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata da karfe 2 na rana a dakin taro na Africa House da ke gidan Gwamnatin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *