TUC ta gargaɗi gwammatin tarayya da ta guji janye tallafin man fetur

Ƙungiyar ƙwadogo ta TUC a Najeriya ta gargaɗi gwammatin tarayya da ta guji janye tallafin man fetur a daidai wannan lokaci da ta ce talakawan ƙasar na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.

Ƙungiyar na ganin idan har gwamnatin ta janye tallafin farashin man, to hakan zai ƙara wa jama’ar ƙasar ɗimbin wahalhalu da kuma matsin tattalin arziki.

Abin da kuma ita ƙungiyar ta TUC ke cewa ba za ta amince da shi ba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Kwadago ta TUC Kwamared Nuhu Toro ya ce babu yadda za a yi a cire tallafin ba tare da an zauna an tattauna batun cire tallafin tsakanin masu ruwa da tsaki ba.

Ya ce matuƙar aka cire tallafin man to farshinsa zai yi tashin gwauron zaɓi, abin da kuma zai shafi farashin sauran kayayyaki a ƙasar nan.

Kwamared Toro ya ce cire tallafi ba shi ne mafita wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *