Bashir Magashi: “Zamu cigaba da inganta walwala da horar da sojoji”

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da inganta walwala da horar da sojoji.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a Abuja ranar Juma’a, ta hannun Mohammad Abdulkadri, mataimaki na musamman ga ministan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a. kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar Abdulkadri, Magashi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana guda a makarantar horas da sojoji ta Najeriya.

Ministan ya kuma lura cewa jin dadi da horas da sojoji shi ne babban abin da gwamnatin tarayya ta sa a gaba.

Ya yabawa mahukuntan NDA da su canza cibiyar tare da samar da ingantattun ababen more rayuwa.

Kwamandan, NDA, Manjo Janar Ibrahim Yusuf, yayin da yake godiya ga ministan, ya ce ayyukan da ake gudanarwa a cibiyar sun inganta tsarin tsaro na makarantar.

Yusuf ya kuma yabawa babban hafsan tsaron kasa, Gen. Leo Irabor da Shugabannin ma’aikata don tallafin da suke bayarwa ga Cibiyar.

Kafin ya bar Kaduna ministan ya dauki lokaci ya duba layin samar da harsasai na “B” na hukumar kula da masana’antun tsaro ta Najeriya (DICON) da gobara ta kone a makon jiya.

Darakta-Janar na DICON, Manjo Janar Hassan Tafida, shi ma ya jagoranci ministan da hafsoshin ma’aikatan zagaye na ORDFAC “E” 7.62 X39 Special Production line. (NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *