Zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake fitar da gargadi ga masu bayar da bashi ga gwamnatin Ganduje.
Duk ku tsaya cak cikin tunatarwa zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da shawarar dakatar da basussuka ga masu ba da lamuni na gida da waje.
Ya bukace su da kada su karbi wata bukatar bada lamuni ba tare da yardarsa ba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Abba Yusuf ya bayar da irin wannan shawara kan gine-gine ba bisa ka’ida ba a wurare mallakin gwamnati da na taruwar jama’a.
Sai dai kuma gwamnatin Ganduje ta yi gaggawar mayar da martani kan wannan shawara, inda ta tunatar da shi cewa har yanzu suna kan karagar mulki don haka ya jira har sai ranar 29 ga watan Mayu.
Amma a cikin nasiha ta biyu dake kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan mai jiran gado Sanusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya nace cewa shawarar ta zama dole.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Daga ranar 18 ga Maris zuwa 29 ga watan Mayu, babu wani mai ba da lamuni (na gida ko na waje) da zai amince da bayar da rance ga gwamnatin jihar Kano ba tare da amincewar gwamnati mai zuwa ba.
“Duk irin wannan wurin ba da lamuni da aka amince da kuma bayar wa Gwamnatin Jihar Kano tsakanin ranar zaɓe da ranar rantsar da shi ba tare da saninsa ba da kuma amincewar gwamnati mai zuwa ba sabuwar gwamnati baza ta karrama shi ba.
“Duk masu ba da rancen kuɗi ga Gwamnatin Jihar Kano za su lura cewa duk sharuɗɗa da ka’idoji duk wuraren lamuni da ake da su sai.an sake shawarwari da sabuwar gwamnati ta hanyar bincikar amfani da kowane lamuni.”
Lallai wannan hakane kar aje a gadawa kanawa bashi aka.