Ngige: “Ya kamata Tinubu ya duba batun albashi”.

Ministan kwadago da samar da ayyuka a Najeriya, Chris Ngige ya ce ya kamata zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya duba batun albashi.

Tashar talabijin Channels ta rahoto Dr. Chris Ngige yana cewa yanada kyau da zarar Bola Tinubu ya shiga ofis, gwamnatinsa ta fara shirin kara albashin ma’aikata.

Da aka yi hira da shi, Ministan tarayyan ya ce akwai bukatar gwamnati mai zuwa ta kara mafi karancin albashin kasar daga N30, 000.

A tattaunawarsa da gidan talabijin, Ngige ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince ayi wa manyan ma’aikata karin albashi daga Junairun 2023.

Rahoton ya ce Ministan ya tabbatar da an yi tanadin karin a cikin kasafin kudin bana, ya ce hakan zai rage radadin tsadar rayuwa da tashin farashi.

Ngige yana ganin zai yi kyau duk bayan shekaru biyar, gwamnatin
Najeriya ta duba albashin ma’aikata, ayi la’akari da halin rayuwa a
daidai lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *