Matawalle ya zargi gwamnatin tarayya da shirya masa makarkashiya a zabukan da suka gabata

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi gwamnatin tarayya da shirya masa makarkashiya a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, domin hukunta shi kan kalubalantar sabon tsarin CBN kan sauya fasalin kudi.

Gwamna Matawalle da takwarorinsa na Kano da Kaduna, Abdullahi Ganduje da Nasir El Rufa’i sun shigar da kara suna kalubalantar gwamnatin tarayya da babban bankin Nijeriya CBN a kotun koli kan sabon tsarin sauya fasalin Naira.

Matawalle dai ya sha kaye a zabensa na sake tsayawa takara a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal.

Lawal ya samu kuri’u 377,726 inda ya doke Matawalle wanda ya samu kuri’u 311,976.

Shi ma dan takarar APC a Kano ya sha kaye a zaben gwamna amma El-Rufai ya samu nasara a Kaduna.

Sai dai a wata hira da ya yi da gidan rediyon DW na tsawon mintuna tara, gwamna Matawalle ya ce an gargade shi da cewa, zai samu matsala a zabensa.

Ya ce, an aika sama da motoci 300 dauke da sojoji zuwa jihar a jajibirin zabe tare da tura sojoji sama da 50 zuwa rumfunan zabe don tsoratar da masu kada wa APC kuri’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *