Masari: “Tinubu Addu’a Yake Bukata Daga ‘Yan Najeriya”

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya roki ‘yan Najeriya da su kara yiwa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu’a. Masari, a lokacin wani taro na musamman ya.

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya roki ‘yan Najeriya da su kara yiwa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu’a.

Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Masari, yayin wani taro na musamman na buda baki da addu’o’i da aka shirya a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Katsina, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da jam’iyyar APC ta samu a babban zaben kasar nan.

A cewar gwamnan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito zababben shugaban kasa yana shirya taron addu’o’i duk shekara a cikin watan Ramadan.

Ya ce, “Taron na bana an shirya shi ne na musamman domin godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar da muka samu a zabukan da aka gudanar a kasar nan.

“Ba abin da za mu iya sai godiya ga Allah bisa nasarar da aka samu a Katsina da Najeriya baki daya.

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka zo nan tare da shugabannin addinai, shugabannin gargajiya, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

“Yanzu shi ne zai zama sabon shugaban kasa, don haka yana bukatar karin addu’a. Alhamdulillahi mutane sun gane cewa bayan zaben shugabanni, dole ne a yi addu’a a gaba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *