An bukachi kingiyoyi masu zaman kasu da su cigaba da tallafawa AKTH

An bukachi kingiyoyi da kamfanoni masu zaman kasu da su cigaba da tallafawa asibitin koyarwa na Malam Aminu dake nan kano, harma da sauran cibiyoyin lura da lafiya a jaharnan.

Shugaban asibitin na mala Aminu kano Farfesa Abdurrahaman Abba sheshe. Shine yayi wannan kiran a yayin taron kaddamar da wata ciya da wani kamfani ya samar a asibitin.

Farfesa Sheshe ya kara da cewa an samar da sashin domin masu fama da larurar fyarfyadiya da chutar rawar jiki da kuma kananan yaran da suka samu nakasa da dadai sauran su.

A nasa jawabin Daraktan kamfanin Injiniya Dakta Rabiu sulaiman ya bayyana dalilin su na samar da cibiyar da irin muhimmmancin da al’umma musamma marasa galifu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *