INEC Ta Bai Wa Abba Shaidar Lashe Zaben Gwamnan Kano

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bai wa Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP takardar shaidar lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Abba ya kayar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta ki amincewa da sakamakon zaben, inda ta bukaci INEC da ta sake duba sakamakon zaben.

Hakan ya sanya jam’iyyar shiga zanga-zanga a satin da ya gabata, amma INEC ta ce su garzaya kotu don neman hakkin da suke ikirari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *