Akwai Yiwuwar Samun Karin Kudin Kujerar Aikin Hajjin Bana

A dai-dai lokacin da hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON ke cigaba da shirye- shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 cikin nasara rahotanni na nuna yuwar samun karin kudin kujerar zuwa aikin hajjin bana fiye da yadda aka samu a bara sakamakon karin kudin masauki da alhazai zasu iya fuskanta a kasar Saudiia.

Binciken da jaridar Hajj Reporters ta gudanar ya bayyana cewar kasar Saudi Arabia ta rushe wasu daga cikin masaukan da alhazai ke sauka domin kawatasu da hakan ka iya shafar farashin masaukin da alhazan za su sauka a wannan shekara.

Kazalika binciken ya gano cewar kusan mahajjata miliyan uku ne ake saran za su gudanar da aikin Hajji a wannan shekara ta 2023 fiye da yadda na shekarar 2023 da hamajjata miliyan daya ne suka gudanar da aikin Hajjin sakamakon matakin da kasar ta dauka akan dakile yaduwar cutar Korona.

Jaridar Hajj Reporters ta rawaito cewar a yanzu haka masaukin alhazan jihohin Kano, Sokoto, Katsina, Kaduna, Bauchi, Kwara, Plateau ke samu da araha tuni Kasar ta Saudi Arebia, ta mayar dashi gurin yawon bude idanu,

A yanzu haka dai tuni Hukumar aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta dauki matakin tura tawaga ta musanman zuwa kasar ta Saudi Arebia Karkashin jagorancin Kwamishinanta mai kula da harkokin kudi da ma’aikata Alhaji Nura Hassan Yakasai, domin tabbatar da cewar Alhazan Najeriya sun samu masauki mai sassauci da zai sa a samu rangwame a kudin kujerar zuwa aikin Hajjin a wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *