Mustapha: “Buhari ba zai kara ko kwana daya ba a kan mulki”.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai kara ko kwana daya ba a kan mulki.

Bayan kammala zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, ana sa ran Buhari zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, Mustapha, shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa, ya ce ana nan ana ta kokari don ganin ba a samu tangarda ba wajen mika mulkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *