Karancin Naira: NLC ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar

Kungiyoyin Kwadago na Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suka shirya fara a gobe Laraba, sakamakon karancin kudin Naira.

Kungiyoyin kwadagon sun bayyana haka ne a taron majalisar zartarwa ta kasa a ranar Talata.

Ku tuna cewa kungiyoyin kwadagon sun yi barazanar fara yajin aiki a fadin kasar nan daga ranar Laraba 29 ga Maris, 2023 idan har gwamnati ba ta magance batutuwan da suka hada da karancin takardun naira, karancin man fetur da karin kudin wutar lantarki ba.

Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya ce bayan karbar bayanai daga majalisun ta na Jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, NLC ta yanke shawarar dakatar da shirin zaman gida da aka shirya yi wa ma’aikata a makon jiya.

Ya ce kungiyar NLC za ta dawo da zanga-zangar da aka shirya idan ‘yan Najeriya ba su samu kudin Naira nan da karshen mako biyu ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, suka gana da shugabannin majalisar a wani yunkuri na dakile yajin aikin da ke gabatowa.

A wajen taron, Emefiele ya ce an dauki matakin rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta dangane da tabarbarewar Naira a kasar.

Shugaban babban bankin ya ce an samar da makudan kudade ga bankunan kudaden ajiya kuma an umarce su da su bude rassansu a ranakun Asabar da Lahadi kuma sun bi umarnin da babban bankin na CBN ya basu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *