Buhari Zai Bude Wajen Hakar Mai Na 3 A Yankin Arewa

A Gobe Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da tashar mai ta uku a Arewacin Najeriya.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (Nigerian National Petroleum Corporation Limited) ta fitar a ranar Litinin da ta gabata.

Rijiyar mai tana garin Ebenyi a hedikwatar karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

An shirya budewar ne tunda fari a ranar Talata, 28 ga Maris, 2023.

Ita ce rijiyar mai ta biyu a yankin Arewa ta tsakiya; ta farko itace ta Ibaji a jihar Kogi.

A tarihin hako man Najeriya, rijiyar mai na Ebenyi ita ce ta uku a Arewacin Najeriya; ta farko itace ta Kolomani, wanda take a cikin yankin Bauchi/Gombe.

A ranar 15 ga watan Janairun 1956 ne Najeriya ta fara gano danyen mai a matsayin wata hanyar kasuwanci a Oloibiri, cikin al’ummar yankin Neja Delta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *