Rundunar ‘yan sanda ta kama mutum 781, kan laifukan da suka shafi zaɓe

Rundunar ‘yan sandan kasarnan tace ta kama mutum 781, kan laifukan da suka shafi zaɓe a lokacin zaɓukan ƙasar na shekarar 2023.

Babban sufeton ‘yan sandan ƙasar Usman Baba Alkali ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasar 36, tare da wasu manyan jami’an ‘yan sandan.

Yayin da yake cikakken bayani game da kamun, Alkali Baba yace an aikata laifukan zaɓe 145 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda rundunar ta kama mutum 203.

Sai kuma a lokacin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jihohi inda rundunar ta ce an aikata laifuka 304, lamarin daya sanya rundunar ta kama mutum 578.

Babban sufeton ‘yan sandan ya ce rundunar ta shirya ganawa da babban sufeton da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasarnan da kuma sauran manyan jami’an ‘yan sandan, don tattauna barazanar da tsaron ƙasar ke fuskanta.

Wanda a cewarsa ‘yan siyasa ke ƙoƙarin tayar da hatsaniya a ƙasar bayan zaɓukan ƙasar da suka gabata.
Ya kuma yi Allah wadai da ‘yan siyasar da suke ƙoƙarin tayar da hargitsi ta
hanyar tunzura jama’a domin cimma wasu muradunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *