NiMet ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a fadin wasu jihohin kasar.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a fadin wasu jihohin kasar.

Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.

Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci karuwar yanayi na zafin rana sun hada da Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.

Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benuwe da Bauchi da Gombe da kuma Borno.

A cikin wata sanarwa da NiMet ta fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce hukumar ta lura da cewa yanayin zafin rana zai kai maki 40 a ma’aunin celcius a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

NiMet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun hada da wasu sassan Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.

NiMet ta yi gargadin cewa jihohi kamar a Bauchi da Gombe da kuma Adamawa na cikin hadarin rashin jin dadi musamman a bangaren lafiyarsu.

Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.

Ta kuma shawarci masu azumi da kar su rika fita cikin ranar, sannan kuma su rika shan wadataccen ruwa a lokatan shan ruwa da sahur.

Hukumar ta NiMet ta kuma tabbatar wa mutane cewa za ta ci gaba da bibiyar yanayi don sanar wa al’umma halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *