INEC Ta Sanya Ranar Gudanar Da Zabukan Cike Gurbi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar gudanar da zaben cike gurbi na Yan Majalissun tarayya, na jiha da kuma Gwamnoni a wasu jihohin.

INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a shafinta na Facebook.

INEC ta ce za a gudanar da dukkanin zabukan cike gurbin ne a ranaar 15 ga watan Afurilun shekarar 2023.

Sai dai INEC ba ta yi cikakken bayani ba kan gudanar da zaben, inda kuma ta ce, za ta yi karin haske nan ba da jima wa ba.

Idan ba amanta ba, Jami’an tattara sakamakon zabe a jihohin Kebbi da Adamawa da dai sauransu sun bayyana zabukan Gwamnonin jihar a matsayin wadanda ba su kammalu ba.

Kana a zaben da aka gudanar na ranar 25 ga watan Maris din shekarar nan, Jami’in tattara sakamakon zabe dake yankin Kebbi ta Arewa ya bayyana zaben dan majalissar Dattijan yankin a matsayin wanda bai kammalu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *