Kungiyar SERAP, ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da ta binciki wasu gwamnonin Jihohi da mataimakansu kan zargin bangar siyasa da siyan kuri’u a zaben da aka kammala.
SERAP, wacce ta yi wannan kiran a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, ta kuma bukaci INEC ta nada wani kwamitin shari’a mai zaman kansa da zai binciki zargin tashe- tashen hankula da sauran laifukan karya dokar zabe da ake yiwa wasu masu rike da mukaman siyasa.
Kungiyar mai zaman kanta, a cikin wasikar data aikewa shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ta kara yin barazanar gurfanar da hukumar zabe gaban kotu idan har bata binciki wadanda ake zargi da aikata laifuka da masu daukar nauyinsu da suka aikata miyagun laifuka a lokacin
zaben ba, kuma a gurfanar da kowaye a gaban kuliya tare da hukunta shi.