PDP ta dakatar da Iyorchia Ayu

Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da shugabanta na ƙasa, Iyorchia Ayu bisa zargin sa, da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka ɗauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri’ar rashin ƙwarin gwiwa kan ayyukansa.

A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasa da Ayu da kuma na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki ɗaya, a zaɓen gwamna.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kuɗaɗen da ake karɓa na shekara-
shekara daga ƴaƴan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.

Shugabannin PDP a gundumar, su 12 daga cikin 17 ne suka sanya hannu
kan takardar dakatar da shugaban na PDP.
Sun kuma yi zargin cewar Ayu bai kaɗa ƙuri’a ba a lokacin zaɓen gwamna da
na ƴan majalisar dokokin jiha da aka gudanar a 18 ga watan Maris, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *