Mataimakin Abacha, Laftanar Janar Oladipo Diya ya rasu.

Tsohon mataimakin shugaban rundunar sojin Najeriya a zamanin mulkin janar sani Abacha, Laftanar Janar Oladipo Oyeyinka Diya ya rasu.

Oladipo Diya wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a zamanin mulkin sani Sani Abacha, a cikin watan Afrilu mai zuwa ne zai cika shekara 79 a duniya.

A wata sanarwa da ɗansa Barrister Oyesinmilola Diya, ya fitar a madadin sauran iyalansa, ya tabbatar da mutuwar tsohon babban jami’in sojin da safiyar ranar Lahadi.

An dai haifi Janar Oladipo Diya a garin Odogbolu na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, yana daga cikin dakarun da suka yi yaƙin basasar ƙaras, kafin ya zama babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar,
a shekarar 1993.

Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar a shakerar 1994.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *