Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce za ta raba takardun shaidar nasara ga duka wadanda suka lashe zaben Gwamnoni a kasar nan.
A wata sanarwa da ta fitar a daren jiya, INEC ta ce za a mika\ satifiket ga zababbun gwamnoni da wadanda suka lashe zaben majalisar dokoki.
Kwamishinan yada labaran hukumar festus okoye ne ya bayyana hakan inda yace za a fara wannan aiki ne daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2023 da muke ciki, a ofisoshin hukumar INEC da ake dasu a jihohi.
Sashe na 72 (1) ya wajabtawa hukumar kasar bada takardar shaida ga ‘yan takaran da suka yi nasara, za ayi hakan ne kafin a zarce kwanaki 14.
A dalilin haka, Okoye ya ce daga ranar Laraba zuwa Juma’a mai zuwa, zababbun Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha za su karbi takardar nasararsu.