Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya musanta cewa an kai wa gidansa hari a jihar Bauchi.
Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban Hukumar ta INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, ne ya bayyana hakan a karshen makon nan.
A wata sanarwa da ya fitar yace Farfesa Yakubu bai mallaki wadannan kadarorin ba, ko dai a Bauchi ko kuma a wani wuri ba.
Daily Trust a ranar Lahadin nan ta rawaito cewa wani faifan bidiyo na harin da aka kai gidan wani fitaccen mawaki a jihar Kano, Rarara, ana yiwa lakabi da gidan shugaban INEC.
“Kadarar da ake zargin wasu matasa ne suka kai wa hari a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ba na shugaban INEC ba ne. Ba shi da dukiyar da ake magana a kai a Bauchi ko ma a fadin duniya.’’ in ji Oyekanmi.
Gwamnatin tarayya ta kammala ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara guda 1,375 a fadin kasar nan wadanda suka lashe kudi naira biliyan 45.89 cikin shekaru ukun da suka gabata, kamar yadda sabon alkalumman da hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta tattara ya bayyanar.
Bayanai daga hukumar sun nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar dake kula da samar da wutar lantarkin, ta gudanar da ayyukan ne ta hanyar bunkasa karfin wutar lantarki ta kasa, da kara yawan kananan tashohin lantarkin, da samar da fitulun kan titi, da sauran su.