PDP ta dakatar da Shema, Fayose da wasu bisa zargin yi mata zagon kasa

Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar PDP ta kasa, ya dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema da na Ekiti, Ayo Fayose, bisa zarginsu da yi wa jam’iyyar zagon kasa. 

Kazalika jam’iyyar ta kuma dakatar da tsohon sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim da wasu mutum biyu.

Kwamitin ya ce ya mika lamarin Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ga kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Fayose dai a wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an hange shi yana nuna jin dadinsa kan yadda PDP ta sha kaye a zaben Gwamnan Jihar Sakkwato.

Sai dai bidiyon ya tada kura, inda mutane da dama a jam’iyyar suka dinga cece-kuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *