Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emiefele, ya roki afuwar ƴan Najeriya kan matsalar da ake fuskanta wajen tura kuɗi ta intanet.
Emefiele ya bayyana haka ne a taron kwamitin tsare-tsare kan harkokin kuɗi da aka gudanar a Abuja, inda ya tabbatar wa ƴan ƙasar cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.
A cewarsa, sashin da ke kula da biyan kuɗaɗe na babban bankin, ya yi iya kokarinsa don tabbatar da cewa an magance matsalar, a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar wahalhalu wajen aika kuɗi da wayoyinsu da kuma a na’urar cirar kuɗi ta POS.
An soma fuskantar matsalar ne tun bayan da gwamnati ta kaddamar da batun sake fasalta kuɗi wanda kuma ya janyo ƙarancin takardun kuɗi a faɗin ƙasar.
A taron, gwamnan babban bankin ya kuma yi magana kan rashni wadatuwar takardun kuɗi a ƙasar saboda sake fasalin naira, inda ya ce bankin zai ci gaba da buga sabbin takardun kuɗi domin su wadatu musamman ma a kasuwanni.