Buhari ya gargadi ’yan kasuwar da ke kara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ’yan kasuwar da ke kara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi da su daina saboda ya saba da koyarwar Musulunci.

Ya bayyana haka ne ranar Laraba, a cikin sakonsa ga al’ummar Musulmi kan shiga watan Ramadan da aka fara ranar Alhamis.

Buhari, ya kuma shawarci Musulman Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan dabi’un addinin Musulunci a mu’amalolinsu, ba wai kawai a baki ba.

Sanarwar, wacce Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayyana kyawawan dabi’un Musulunci irin su tausayi da kaunar juna.

A ranar Alhamis ce Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na sauran sassan duniya domin fara azumin watan Ramadan, bayan an ga watan a wurare da dama na kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *