Birtaniya za ta saka wa waɗanda suka aikata laifukan zaɓe a Najeriya takunkumi

Ofishin jakadancin Biritaniya a Najeriya ya ce ƙasar za ta hukunta ko saka wa duk wani da aka samu da aikata laifi loakcin zaɓe takunmi.

Karamin ministan raya ƙasashe na Birtaniya, Andrew Mitchell ya ce ƙasar a shirye take da ta ɗauki mataki kan wadanda suka tayar da rikicin zaben da aka kammala.

Hukumar ta ce Burtaniya ta riga ta tattara sunayen waɗanda suka aikata laifin kuma za ta sanya takunkumi, ciki har da hana su samun bizar ƙasar a karkashin tsarin takunkumin kare hakkin ɗan Adam.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta ce, “Za mu iya tabbatar da cewa muna tattara bayanan da suka dace, da nufin ɗaukar mataki kan wasu mutane.

Ofishin ya ce ya tura masu sa ido zuwa jihohi shida, inda ta ce an lura da cewa akwai matsala a wuraren.

“Mambobin tawagar mu na sa ido sun lura da tashin hankali da tsoratar da masu zaɓe a wurare da dama lokacin kaɗa kuri’a,” in ji sanarwar.

Ofishin jakadancin na Birtaniya ya ce ya samu rahotanni da suka tabbatar da cewa an batutuwan sayen kuri’a da sace kayan zaɓe da kuma kawo cikas ga harkokin zaɓe a jihohi da dama da suka haɗa da Legas da Eugu da kuma Ribas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *