An Samu Ekweremadu, Matar Sa Da Laifin Safarar Sassan Jikin Mutumn

Wata kotu ta samu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice da laifin yin safara da kuma cire sassan jikin dan adam a kasar Ingila.

Wani alkali ya gano cewa Sanata Ike Ekweremadu, mai shekaru 60, matarsa ​​Beatrice, mai shekaru 56, da kuma “ma’aikacin tsakiya” Dokta Obinna Obeta, mai shekaru 50, sun kasance da laifin hada baki wajen kawo wani matashi kasar Biritaniya domin bayar da kodarsa bayan yin gwaji na makonni shida.

‘Yar su Sonia, mai shekaru 25, ta yi kuka yayin da aka wanke ta daga wannan tuhuma a ranar Alhamis.

An ce sun hada baki ne da laifin kawo matashin mai shekaru 21 mai sana’ar siyar da kayayyaki akan titin Legas zuwa Landan domin yin amfani da kodarsa, kamar yadda alkalan kotun suka gano.

Wanda abin ya shafa, dan shekara 21 mai sana’ar sayar da kayyaki akan titin Legas, an kawo shi kasar Burtaniya a shekarar da ta gabata don ba wa Sonia kodarsa a wani dashen kansa na fam 80,000 a asibitin Royal Free Hospital da ke Landan.

Gwamnatin jihar Kaduna na samun sahihan rahotannin sirri da ke bayyana shirin da wasu ‘yan siyasa ke yi na daukar nauyin da kuma tunzura mabiyansu kan ayyukan da ba su dace ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *