Sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulman kasar da su fara duba jinjirin watan Ramadana da yammacin ranar Laraba.
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da daraktan tafiyar da harkokin Majalisar Koli , Arc. Zubairu Haruna Usman Ugwu.
A cewar sanarwar, an yanke shawarin hakan ne a wani zama da kwamitin duban wata na NMSC, inda shugaban kwamitin ya bukaci Musulmi su tuna cewa, ranar Laraba ce 29 ga watan Sha’aban na Hijira 1444.
A cewar kwamitin, idan aka ga watan a gobe Laraba, za a tashi da Azumin watan Ramadana a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris 2023, kamar yadda ake sa ran Sarkin Musulmi zai sanar.
Idan ba a ga watan ba, Zubairu ya ce, ranar Juma’a 24 ga watan Maris ce za ta zama ranar 1 ga watan Ramadana a wannan shekarar.
A bangare guda, kwamitin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su koma ga Allah tare da yiwa kasar addu’o’i masu amfani a watan mai alfarma.