Jam’iyyar APC a jihar Bauchi, ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar wanda ya bai wa Bala Mohammed na jam’iyyar PDP wanda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar cewa ya lashe a karo na biyu.
A taron manema labarai da ta kira ranar Litinin, ɗan takarar jam’iyyar Air Marshal Sadiq Baba Abubakar mai ritaya ya ce an tafka kura-kurai a zaɓen da dama waɗanda suka tilasta wakilan jam’iyyar ƙin sanya hannu kan takardar shaidar sakamakon zaɓen.
Jam’iyyar APC a jihar ta yi zargin cewa an tabka maguɗi bayan kura-kurai da ta yi zargi an samu, don haka ta buƙaci hukumar zaɓen ƙasar ta soke sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin Alƙaleri da Kirfi da Toro da Warji da Zaki.
Sannan ta bukaci bayan soke zaɓen, a kuma bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.
Air Marshall Abubukar Baba Sadique mai riyata ya yi zargin cewa an razana mutane da makamai, sannan ya yi zargin cewa jam’iyyar PDP ta sayi ƙuri’u a rumfunan zaɓen.
Ya ce wakilan jam’iyyarsu sun ƙi saka hannu a kan sakamakon da suka yi zargin an tafka maguɗi, amma duk da haka an sanar da sakamakon zaɓen.
Sannan ya ce za su yi nazari da kuma tattaunawa da al’ummarsu kan sakamakon zaɓen kafin ɗaukar mataki na gaba.