Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana fita A duk fadin jihar

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da sanya dokar hana fita a duk fadin Jihar daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Matakin na zuwa ne bayan an ayyana sakamakon zaben Gwamnan Jihar, inda Gwamna mai ci, Bello Matawalle na APC, ya sha kasa a hannun dan takarar PDP, Dauda Lawal Dare.

A cewar wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Dosara ya fitar ranar Talata, ya ce sun dauki matakin ne la’akari da yadda mutane suka bige da lalata dukiyoyi da sunan murnar cin zabe.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Zamfara ta lura da abin takaici na yadda ake lalata kadarorin gwamnati da na daidaikun mutanen da ba ruwansu, da sunan murnar cin zaben da aka bayyana jiya.

“Rahotannin da muka samu sun nuna cewa an sami asarar rayuka, an kone gidaje sannan an farfasa shaguna.

“Saboda mu yi wa tufkar hanci, gwamnati ta yanke shawarar sanya dokar hana fita a duk fadin Jiha daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

“Muna ba jami’an tsaron umarnin su tabbatar da an bi wannan dokar yadda ya kamata,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *