Amurka Za Ta Sanya Takunkumin Hana Biza Ga Masu Magudin Zaɓe A Najeriya

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa zata sanya takunkumin shiga kasar ga wasu mutane kan zaben da aka gudanar a Najeriya

Gwamnatin Amurka ta ce za ta kakaba takunkumin biza da kuma matakan da ake da su a kan wadanda suka yi zagon kasa a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a ranar 18 ga Maris.

Rahma ta tattaro cewa Ma’aikatar hulda da jama’a ta ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta bukaci hukumomin Najeriya da su bi diddigin lamarin tare da gurfanar da duk wani mutum da aka samu ya bayar da umarni ko aiwatar da yunkurin tursasa masu kada kuri’a da kuma dakile kada kuri’a a lokacin gudanar da zaben.

Sanarwar ta kara da cewa, “Najeriya ta gudanar da zagaye na biyu na tsarin zabenta tare da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 18 ga watan Maris.

“Amurka ta damu matuka game da munanan ta’addanci da kuma murkushe masu kada kuri’a da aka yi a lokacin zaben a Legas, Kano da sauran jihohi.

“Mambobin ofishin diflomasiyyar Amurka sun lura da zabukan da aka yi a Legas da sauran wurare kuma sun gane wa idanunsu wasu abubuwan da suka faru.

“Yin amfani da kalaman kabilanci kafin zaben gwamna da kuma bayan zaben gwamna a Legas ya shafi batun.

“Muna yaba wa dukkan ‘yan siyasar Najeriya, shugabannin addini da shugabannin al’umma, matasa, da ‘yan kasa da suka zabi kin amincewa da kuma yin magana kan irin wannan tashin hankali da kalamai masu tayar da hankali, tare da tabbatar da kudurin ‘yan Najeriya da mutunta tsarin dimokuradiyya.

“Muna kira ga mahukuntan Najeriya da su bi diddigin lamarin tare da gurfanar da duk wanda aka samu da yin umarni ko aiwatar da yunkurin tursasa masu kada kuri’a da murkushe zabe a lokacin gudanar da zabe.

“Amurka kuma za ta yi la’akari da duk wasu matakan da ake da su, gami da ƙarin takunkumin visa, kan mutanen da aka yi imanin cewa suna da hannu, ko kuma suna da alaka a lalata tsarin dimokuradiyya a Najeriya.”

A cewar Ofishin Jakadancin, bayan zaben kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Amurka ta bi sahun sauran masu sa ido na kasa da kasa wajen yin kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta inganta harkokin zabe da kuma abubuwan fasaha da suka samu kura-kurai a wannan zagayen zaben.

An ruwaito cewa Ofishin Jakadancin ya bayyana cewa, zaben na ranar 18 ga watan Maris ya kasance kamar an samu ingantuwar aiki sosai, domin an bude rumfunan zabe a kan lokaci, kuma galibin sakamakon da aka samu ana ganinsu ta hanyar kallon a shafin yanar gizo a kan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *