Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Uba Sani, ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kaduna.
Baturen zaɓen jihar Kaduna kuma shugaban jami’ar Usmanu Dan Fodio Sokoto, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, shine ya bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Uba Sani ya samu ƙuri’u 730,002 inda ya doke abokin takarar sa mai biye da shi, Isa Ashiru Kudan, na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu ƙuri’u 719,196.
Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Jonathan Asake, ya zo na uku inda ya samu ƙuri’u 58,283 yayin da ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Suleiman Hunkuyi ya samu ƙuri’u 21,405.