Gwamnatin Kano Ta Sanya Dokar Hana Fita

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana zirga zirga a Jihar Kano daga safe zuwa yamma.

Kwamishinan Watsa Labarai, Muhammad Garba ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano, cewa sanya dokar ya zama dole saboda guje wa karya doka da oda duba da irin damuwar da aka shiga a lokacin tattara salamakon zaben gwamnan jihar.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa dan takarar gwamna a Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ne ya lashe zaben gwamnan jihar.

Mataimakin gwamna mai ci, Nasir Yusuf Gawuna, ya zo na biyu, a zaben, wanda kafin sanar da sakamakonsa aka yi ta jira da kananan maganganu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *